🧕HIJJABI NA MUMINAI MATA NE 12🧕
🧕NAGARTAR HIJJABI A GURIN ƳA MACE🧕
HIJJABI IMANI NE:* Allah be saukar da ayoyinsa akan hijjabi ba sai ga muminan mata, shiyasa ya ce: “Al muminatu" be ce taron mata duka ba. A gurare da yawa cikin Qur'ani Allah yana magana ne akan “Mata Muminai”.
🧕Nana Aisha, matar Annabi (ﷺ), tayi magana da wasu mata da suka zo daga Banu Tamim don su ziyarce ta da kaya sharashara a jikinsu, sunyi shiga wacce take bata dace ba, sai ta ce musu: “Idan har ku muminan mata ne, to gaskiya wannan ba itace shigar matan muminai ba, amma idan ku ba mata muminai ba ne to ku bar abin ku.”
🧕HIJJABI KUNYA NE GARE KI Akwai hadisai guda biyu ingantattu da suke nuni akan: "Ko wane addini yana da halin kirki kuma halin kirkin musulunci shi ne kunya “hayah” kuma Kunya daga imani take, kuma imani yana cikin aljanna.”
HIJJAB YANA SA MUMINAN MAZA SU YI KISHINKI: Hijjabi yana sa miki farin jini, yasa miki ƙwarjini ki ɗinga burge masu imani, haka kawai se mutum yaji yana sonki bacin be taɓa ganinki ba, kawai sabida yadda kike yin kyau cikin liqabinki da hijjabinki. Masu imani muminai se su ji suna yin kishinki, haka kawai se suji kamar tsokar jikinsu ce ke.
🧕Amma shi munafuki tsoro zaki dinga bashi, se ya dinga ganinki wata dodonniya a gabansa, da ya ganki cikin hijjabi da liqabi se yaji kawai yana kyarma kamar ze fita a guje. Ke sheɗan ma tsoronki ze ji wallahi balle kuma muƙarrabansa. Ta bangaren ƴan uwanki mata se ki ga duk wata ƴar iska ma tsoronki take ji, zata iya cewa sauran ƙawayenta ku zo muje muyi shagali amma ke tsoron gayamiki take yi sabida farin jinin *Hijjabi a gurin Musulma mumina.*
🧕Ƴar uwata wannan kadan daga cikin Nagartar masu saka rufe jikinsu kenan, Ni *Abu Khadija* wallahi ina ƙaunar duk wata wacce take rufe jikinta, haka kawai idan naga mace da liqabi da hijjabi se naji ta burgeni kuma ina kaunarta sabida Allah.
🧕Allah ya datar damu, ya tsarkake mana niyyarmu.
✍Rubutawa: Abdullah A Abdullah Abu Khadijat (أنصار السنة)
07/06/1440.
14/02/2019.
Ga masu buqatar shiga Zauren Sawtul hikmah zasu iya bi ta links din da ke ƙasa
+234 8032312988
SAWTUL HIKMAH TAKU CE DOMIN YAƊA SUNNA