YAWAN WASIWASI A CIKIN SALLAH
Tambaya
Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu. Malam ina da tambaya, malam don Allah na kasance ina yawan wasiwasi cikin sallah, don Allah yayazanyi na rabu dashi? Allah yakara lapiya.
AMSA
Wa alaika.
Dan uwa ana iya koran wasiwasi ne gwargwadon yadda sallar ka tayi kusaci da Sallar Annabi, (yadda ya koyar) duk mutumin da sallar sa tayi nesa da sallar Annabi toh fa zai hadu da wasiwasi a cikin sallarsa.
Annabi (S.A.W) yace kuyi salla yadda kuka ga inayi. A cikin salla sai ya koya mana idan munyi Kabbara bayan mun tabbatar mun fuskanci alkibla.
Abu na biyu shine Addu'ar bude salla, ita kuma Addu'ar bude Salla kala- kala ce wacce Annabi ya koyamana, duk wacce ka dauka kayi tayi. Sai dai mafi shahara ko mafi inganci itace wacce ta tabbata cikin bukhari.
Bayan kayi Addu'ar bude salla sai Isti'aza, wacce Annabi ya koyar itace :-
A'UZU BILLAHI SAMI'UL ALIM MINA SHAIDANIR RAJIMI.........
Wannan Isti'aza itace take korar shedan a cikin Sallah idan kayita yadda Annabi (S.A.W) ya koyar.
Daga nan sai Karatun Fatiha, sannan Idonka yana kallon inda zakasa goshinka, ba ka kallon ko ina sai anan sannan tsayuwa mai kyau da karatu mai kyau.
Idan ka tsare wadannan Laduba na salla gwargwadon yadda Annabi ya koyar to gwargwadon yadda zaka rabu da wasi wasi, zata iya yuyuwa Allah ya jarabce ka, duk da ka kare wadancan adab din da abubuwan da ake buqata.
Toh idan wasi wasi yazo maka kana cikin Sallah zaka iya Isti'aza, domin Manzon Allah (S.A.W) yace kayi Isti'aza ka tofa a hagu. Toh in shaa Allahu Sahidan zai tafi ya barka.