DAGA CIKIN LADUBBAN KWANCIYA BACCI (03)
_Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinƙai
5. ƘYAMATAR KWANCIYAR RUB DA CIKI: Yana Daga Cikin Abinda Shari'a take Ƙyamatar Yinsa Yayin Kwanciya Bacci Shine Kwanciyar Rub da Ciki. Ruf da Ciki Kwanciya ce da Akeyi Mutum Ya Kwanta da Cikinsa Bayansa Na Kallon Sama. Kwanciyace ta Ƴan Wuta Shiyasa Ubangiji Maɗaukaki Baya Sonta. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:_
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ، قَالَ: رَأَى رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلًا مُضْطَجِعًا عَلَى بَطْنِهِ فَقَالَ: *(إِنَّ هَذِهِ ضِجْعَةٌ لَا يُحِبُّهَا اللَّه)*
{رواه الترمذي}
_An Karɓo Daga Abi-Hurairah (ra) Yace: *Manzon Allah (ﷺ) Yaga Wani Mutum Kwance Akan Cikinsa, Sai Yace Dashi: “Lallai Wannan Kwanciya Ce Da Allah Baya Sonta".
_(Tirmizi Ya Ruwaitoshi)_
_A Ruwayar Bukhari Kuma *Manzon Allah (ﷺ)* Cewa Yayi:_
*(إِنَّمَا هَذِهِ ضِجْعَةُ أَهْلِ النَّارِ)*
_*“Lallai Wannan Kwanciya Ce Ta Ƴan Wuta".*_
_*6. RUFE ƘOFOFI DA KASHI FITILU DA KAFIN KWANCIYA BACCI:* Yana Daga Cikin Ladubban Kwanciya Mutum Ya Rufe Ƙofar Gida da Ƙofar Ɗaki. Sannan Ka Fitilun dake Ɗakin, Sannan a Rufe Abinci da Duk Abin Sha. Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_
عَنْ جَابِرٍ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ-: *(أَطْفِئُوا الْمَصَابِيحَ بِاللَّيْلِ إِذَا رَقَدْتُمْ، وَغَلِّقُوا الأَبْوَابَ، وَخَمِّرُوا الطَّعَامَ وَالشَّرَابَ)*
(روا لبخاري)
_An Kar6o Daga *Jabir (ra)* Yace: *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Ku Kashe Fitilu Yayin da Kuka Tashi Yin Bacci. Kuma Ku Kukkule Ƙofofinku, Ku Rufe Abinci Da Abin Sha".*_
_(Bukhari Ya Ruwaitoshi)_
_Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba Insha Allah_
*سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لا إِلَهَ إِلا أَنْتَ، أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ*
_*✍🏼Abu Aysha Al-Maliky*_