Shugaban karamar hukumar Sokoto ta Kudu ya jagoranci tarwatsa IFEOMA GUEST inda ake zinace-zinace da 'yan mata kanana, luwadi, shaye-shaye, da sauran miyagun laifukka


Shugaban karamar hukumar Sokoto ta Kudu ya jagoranci tarwatsa IFEOMA GUEST inda ake zinace-zinace da 'yan mata kanana, luwadi, shaye-shaye, da sauran miyagun laifukka 

Shugaban karamar hukumar mulki Sokoto ta kudu Alhajj Farouk Sayudi ya jagoranci tawagar jami'an tsaro tare da dan majalisar jaha mai wakiltar Sokoto ta kudu ta 1 Hon Mustapha Abdullahi Dust domin gani da ido irin yadda matasa ke aikata munanan aiyukkan alfasha da kananan yara mata a IFEOMA GUEST.

IFEOMA GUEST tana daya daga cikin wurare da ake aikata munanan aiyukka tare da bata tarbiyyar yara mata a jihar Sokoto.

Yanzu haka shugaban karamar hukumar Alh Faruk Faruku Sayudi ya isa Police da ke Mabera Mujaya inda ya ke hannun yaran da aka kama ga iyayen su domin su koma gidan iyayen su.

Wani dattijo ya nuna farin cikin sosai tare sa godiya ga shugaban karamar domin ceto 'diyar sa daga wannan hali. 

Akwai wata yarinya daga karamar hukumar Wurno wadda aka hannun ta ga ahugaban karamar hukumar mulki Wurno Hon. Abu Arzika, inda ya bada tabbacin cewa zai gabatar da yarinyar ga iyayen ta.

IFEOMA GUEST ta kasance wurin da matasa ke zuwa da 'yan matan su suna zinace-zinace da su a duk lokacin da su ka bukaci hakan.

Please leave for me a comment

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post