TARIHIN SAHABIL JALIL SULAIMAN BN SARD (RA)*

*TARIHIN SAHABIL JALIL SULAIMAN BN SARD (RA)*




بِسْم الله الرحمن الرحيم



*SUNANSA* SULAIMAN BN SARD BN JUNUN BN ABIL JUNUN BN MUNQIZIL KAZA’iYY.



*ALKUNYARSA* Abu mudrif



*HAIHUWARSA DA WAFATINSA* anhaifeshi shekara ta ashirin da takwas (28) kafin hijra wanda yayi dai dai da shekara ta 594 milady,
Yayi wafati shekara ta 65 bayan hijra muwafiq 685 milady.




*MANZILARSA* Sahabi ne daga cikin sahabban manzon Allah SAW ya musulunta a madina a hannun Annabi SAW, wanda ya kasance sunansa YASAR ayayin da ya musulunta Annabi SAW ya chanja masa suna I zuwa SULAIMAN.



Bayan ya musulunta Yayi musharaka a dukkan yakin da aka gudanar da gwagwarmaya da sahabbai suka sha a zamanin Annabi SAW .



Yana da hadisai da dama daya ruwaito daga Annabi SAW da sayyidna Hassan BN aliyy bn abi dhalib , da Ubayyu BN ka’ab da jubair RA.



Daga cikin wadanda sukayi ruwayar hadisi daga gareshi akwai Abu hanifa da abu abdullahil jadliy da tamim BN salamah RA.



Yana daga cikin mutanen da Sayyidna Hussain BN aliyy BN abi dhalib ya rubuta domin suyi masa mubaya ah , wanda a yakin ne na WARDA da aka gudanar a rabiyyul Akir shekarata 65 bayan hijra aka kasheshi .


Wanda ya kasheshi shine yazid BN Hussain BN namiir ya jefeshi da mashi a kansa bayan fitar ransa ya dauki kansa domin yakaiwa shugabansa Marwan BN hakam.
Yayi wafati yanada shekaru 93 a duniya. *RADHIYALLAHU ANHUM WA RADHU ANH*






✍🏼 *UMM HAMDAN WA HAMEED*






    🎙🎙 *SAUTUL HIKMAH (whatsapp)*





Ga masu sha awar shiga wannan zaure su turo da suna da Address ta wannan numbers 08060027244 / 08039375380.

Please leave for me a comment

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post