*_Darasi na Biyu (2) Karatun Littafin "Tushe Uku na Musulunci"_*
*_Wallafar Limami Muhammad ibn Abdilwahhab_*
_Allah yai masa Rahma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin kai_*
*_Na uku:_* _Cewa duk wanda yayi biyayya ga manzon Allah, kuma ya kadaita Allah, bai halatta yaso wanda ya ke kiyayya da Allah da manzonSa ba, ko da kuwa ya kasance mafi kusancin makusanta gare shi._
*_Dalili kuwa shine fadar Allah Madaukakin Sarki:_*
*لا تَجِدُ قَوْماً يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ يُوَادُّونَ مَنْ حَادَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَوْ كَانُوا آبَاءهُمْ أَوْ أَبْنَاءهُمْ أَوْ إِخْوَانَهُمْ أَوْ عَشِيرَتَهُمْ أُوْلَئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ الْإِيمَانَ وَأَيَّدَهُم بِرُوحٍ مِّنْهُ وَيُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ أُوْلَئِكَ حِزْبُ اللَّهِ أَلَا إِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ*
*_((Ba za ka samu mutane masu yin imani da Allah da ranar lahira su na soyayya da wanda ya saba wa Allah da manzonsa ba, ko da sun kasance ubanninsu ne ko diyansu ko yan uwansu, ko danginsu, wadannan Allah Ya rubuta imani a cikin zukatansu, kuma Ya karfafa su da wani ruhi daga gare shi, kuma zai shigar da su a gidajen Aljannah, koramu na gudana karkashin su, su na masu dawwama a cikinsu. Allah Ya Yarda da su kuma sun yarda da shi, wadannan su ne kungiyar Allah. To, lalle kungiyar Allah su ne masu rabauta.))_*
_Ka sani (Allah Ya shiryar da kai zuwa ga da’arSa), cewa hanya madaidaiciya, hanyar Annabi Ibrahim ita ce: ka bautawa Allah shi kadai, ka na mai tsarkake addini gare Shi;_
_wannan shi ne Allah Ya umurci dukkan mutane, kuma Ya halicce su domin sa,_ *_Allah Ya ce:_*
*وَمَا خَلَقتُ الجِنَّ وَالإِنسَ إِلّا لِيَعْبُدُوِن*
*_((Ban halicci Aljanu da mutane ba sai don su bauta miNi))_*
_Abinda ake nufi da “su bauta miNi” shi ne “su kadaitaNi da ibada.”_
_Kuma babban abinda Allah Yayi umurni da shi shine tauhidi. Kuma ma’anarsa: “kadaita Allah da ibada”._
_Kuma babban abinda Allah Yayi hani da shi shi ne: “Shirka”, ma’anar kuma Shirka: “kiran wani (banda Allah) tare da Shi (Allah)”._
*_Dalili shi ne fadar Allah Madaukakin Sarki:_*
*وَاعْبُدُوا اللَّه وَلاَ تُشرِكُوا بِهِ شَيئا*
*_((ku bauta wa Allah, kada ku hada wani da shi))_*
_Idan a ka ce maka: me ne ne shika-shikai guda uku wadanda ya wajaba mutum ya sansu?_
_Kace: Bawa ya san Ubangijinsa, da addininsa, da Annabinsa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi._
_Idan aka ce maka: Wane ne Ubangijinka?_
_Kace: Allah ne Ubangijina, Wanda Ya rene ni, kuma Ya reni dukkan talikai da ni’imarSa, Shi ne abin bautata, ba ni da wani abin bauta sai Shi._
*_Dalili shi ne fadar Allah:_*
*الحَمْدُ للّهِ رَبِّ الْعَالَمِيْن*
*_((Godiya ta tabbataga Allah Ubangijin talikai))_*
_kuma duk wanda ba Allah ba, shi ake kira taliki, kuma ni daya ne daga cikinsu._
_Idan a ka ce maka: dame kasan Ubangijinka?_
_Sai kace : da ayoyinsa, da kuma halittunSa._
_Daga cikin ayoyinSa, akwai: dare, da wuni da Rana, da Wata, da sammai bakwai, da kassai bakwai da abinda ke cikinsu._
*_Dalili shi ne fadar Allah Madaukaki:_*
*وَمِنْ آيَاتِهِ اللَّيْلُ وَالنَّهَارُ وَالشَّمْسُ وَالْقَمَرُ لَا تَسْجُدُوا لِلشَّمْسِ وَلَا لِلْقَمَرِ وَاسْجُدُوا لِلَّهِ الَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ*
*_((Kuma akwai daga ayoyinSa, dare, da yini,da rana da wata, kada ku yi sujada ga rana,kuma kada kuyi ga wata, kuyi sujada ga Allah wanda ya halitta su, idan kun kasance shine kuke bauta wa.))_*
*_Da kuma fadar Allah Madaukaki:_*
*إِنَّ رَبَّكُمُ اللّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ يُغْشِي اللَّيْلَ النَّهَارَ يَطْلُبُهُ حَثِيثاً وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ وَالنُّجُومَ مُسَخَّرَاتٍ بِأَمْرِهِ أَلاَ لَهُ الْخَلْقُ وَالأَمْرُ تَبَارَكَ اللّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ*
*_((Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda ya halitta sammai da kasa a cikin kwanaki shida, sa annan kuma yadaidaita a kan Alarshi, Ya na sanya dare ya rufe yini, ya na neman sa da gaggawa, kuma rana da wata da taurari horarru ne da umurninsa. To, da halitta da umurni Na sa ne, albarka ta tabbata ga Allah Ubangiji halittu!))_*
_Ubangiji shine abin bauta._
*_Dalili shi ne fadarSa, Madaukaki:_*
*يَأيُّهَا النَّاسُ اعبُدُوا ربَّكُمُ الذَِّي خَلَقَكُم وَالذِّينَ مِن قَبلكُم لَعَلَّكُم تَتَّقُونَ(21) الّذِي جَعَلَ لَكُمُ الأرضَ فِرَاشًا وَالسَّمآءَ بِنآءً وَأنزَلَ مِنَ السَّمَآءِ مَاَءً فَأخرَجَ بِهِ مِن الثَّمراتِ رِزقًا لّكُم فَلاَ تَجعَلُواْ لَلَّهِ أندَادًا وَأنتُم تَعَلُمونَ*
*_((Ya ku mutane! Ku bauta wa Ubangijinku, wanda ya halicce ku, ku da wadanda suke daga gabaninku, tsammaninnku, ku kare kanku! Wanda Ya sanya mu ku kasa shimfida, kuma sama gini, kuma ya saukar da ruwa daga sama, sa annan ya fitar da abinci daga dyan itace game da shi saboda ku. Saboda haka kada ku sanyawa Allah wasu kishiyoyi, alhali kuwa ku na sane._*
_Ibn kathir (Allah Ya rahamce shi) ya ce: Mahaliciin wadannan abubuwa shine ya dace a yi masa Ibada._
_Duka irin dangogin ibadar da Allah yayi umurni dasu a na yin su ne domin Allah, kamar: Islam (Musulunci), da Imani, da Ihsani, haka kuma adua, da tsoro, da fata, da tawakkali, da fata, da fargaba, da kankantar da kai, da maida alamari (zuwa ga Allah), da neman Taimako (daga Allah), da neman tsari, da neman agaji, da yin yanka, da daukar alkawalin yin wata ibada (bakance), dukkan wadannan ibadodin da wasunsu wadanda bamu zana ba._
*_Dalili akan haka shine fadar Ubangiji Madaukaki_*
*وَأنَّ المَسَاجِد لِلَّهِ فَلا تَدعُوا مَعَ اللَّهِ أحَدا*
*_kuma lalle ne wuraren na allah ne , saboda haka kada kukira kowa tare da allah [da su, a cikinsu]._*
*_Mu hadu a darasi Na Uku (3)_*
*🎙Sawtul-hikmah (da'awar sunnah a social media)🎙*
*WhatsApp 📲👇👇*
+2348060027244
+2348039375380
*Official websites 🌍 👇👇*
www.sawtul-hikmah.simplesite.com
*Facebook 💻👇👇*
https://m.facebook.com/sawtulhikmah
Zaku iya cigaba da turo da tambayoyin ku ta email din mu a 👇
Sawtulhikmah01@yahoo.com 📩
Ko ta sabon channel din mu dake you tube..... 🎥
*🎙SAWTUL HIKMAH TAKU CE DOMIN YADA SUNNAH ☝🎙*