Buhari ya yi Allah-wadai da kashe kwamishinan Kimiyya da Fasaha na jihar Katsina

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan kisan da aka yi a jiharsa ta Katsina a ranar Alhamis inda aka kashe kwamishinan kimiyya da fasaha Dakta Rabe Nasir.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya ce kisan kwamishinan mummunan abu ne kuma abin tir ne inda ya ƙara da cewa irin waɗannan mugan ayyukan ba su da mazauni a ƙasar.

Shugaban ya kuma buƙaci jami'an tsaron ƙasar da su gudanar da bincike da kuma tabbatar da cewa an yi hukunci kan waɗanda aka kama da laifi.

Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da matsalar tsaro ta munana.

Ko a jiya sai da ƴan bindiga suka kashe masallata 16 a jihar Neja.

Please leave for me a comment

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post